Hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar Larabar nan cewa, ya zuwa jiya Talata, an yi wa mutane alluran riga kafin annobar COVID-19 sama da biliyan 1.8 a fadin kasar. Kasar Sin dai ta kara daukar matakan hana yaduwar cutar a asibiti, da karfafa yin gwaji, yayin da kasar ke sake samun bullar masu kamuwa da cutar a cikin gida.
Shugaban hukumar lafiya ta kasar Ma Xiaowei, ya bayyana cewa, ya kamata a koda yaushe a ba da muhimmanci ga aikin dakile yaduwar cutar, yana mai gargadi da a kara daura damara wajen yaki da cutar. (Ibrahim)