Sin Ta Cika Alkawarinta Na Ingiza Allurar Rigakafin COVID-19 Zama Hajar Da Ko Wacce Kasa Ke Iya Samu

CRI2021-08-11 13:44:43

Sin Ta Cika Alkawarinta Na Ingiza Allurar Rigakafin COVID-19 Zama Hajar Da Ko Wacce Kasa Ke Iya Samu_fororder_W020210320325482611933

BY CRI HAUSA

Cutar COVID-19 na kan ganiyarta a duniya a bana, wadda ta kawo babbar barazana ga lafiyar bil Adama. Sin tana kokarin cika alkawarinta na ingiza allurar rigakafin COVID-19 da ta zama hajar da ko wacce kasa ke iya samu bisa tunanin shugaba kasar Sin Xi Jinping na “al’ummar bil Adama ta bai daya ta kiwon lafiya”. Ya zuwa yanzu, yawan allurar da Sin ta samarwa kasashen duniya ya kai fiye da miliyan 750, matakin da ya ba da babbar gudunmawa ga gwagwarmayar da duniya ke yi na tinkarar cutar.

A watan Maris na bana, allurar da Sin ta samarwa Colombia a zagaye na uku ta isa Bogotá. Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Ivan Duque Marquez ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo don nuna goyon baya da gaida jama’ar kasar Colombia. Inda ya ce,

“Sinawa kan ce, ‘manyan duwatsu da teku ba su iya raba duk wadanda suke da buri iri daya.’ Sin da Colombia na da daddaden zumunci, duk da cewa akwai teku mai fadi a tsakaninsu, wannan bai hana bunkasuwar huldar kasashen biyu ba ko kadan.”

Ba da dadewa ba bayan barkewar cutar, shugaba Xi Jinping ya yi alkawari a babban taron da kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta shirya a watan Mayun bara, cewar Sin za ta mai da allurar rigakafin ta zama hajar da ko wacce kasa za ta samu ba tare da shiga wani kangi ba idan ta kammala aikin nazari da samar da ita, don baiwa kasashe masu tasowa damar samu cikin sauki. A cikin shekara daya da wani abu da suka gabata, allurar Sin ta samu amincewa daga kasashe fiye da dari 1, musamman ma kasashe masu tasowa, har allurar da Sin ta samar ta zama kaso na farko da wasu kasashen suka samu. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce, allurar Sin ta samarwa kasarsa haske. Yana mai cewa,

“Abokai Sinawa, jama’ar Zimbabwe na namijin kokarin tinkarar cutar, allurar da kasarku ta Sin ta samar wa kasarmu kyauta ta kasance kamar fata mai haske. Muna muku godiya sosai.”

Ban da wannan kuma, a farkon watan Mayun bana, a cikin wayarsa da babban sakataren MDD, Xi Jinping ya jaddada cewa, aikin dake gaban al’ummar duniya yanzu shi ne, yakar cutar cikin hadin kai. Ya ce ya kamata kasashen duniya su hada kansu a maimakon siyasantar da wanann batu. A cewarsa, dole kasashe mafi karfin tattalin arziki su sauke nauyin dake wuyansu don samarwa sauran kasashe kayayyaki. A gun taron koli na kiwon lafiya na duniya da aka yi a ranar 21 ga watan Mayu, Xi Jinping ya sanar da sabbin shawarwarin goyon bayan hadin kai na yakar cutar a duniya, ya ce,

“Sin za ta gabatarwa kasashen duniya tallafin kudi dala biliyan 3 a cikin shekaru 3 masu zuwa, don taimakawa kasashe masu tasowa tinkarar cutar da farfardo da tattalin arziki da rayuwar al’umma. Sin na goyon bayan kamfanonin kasar dake samar da allura da su yi musayar fasahohi da hadin kai wajen samar da allurar da kasashe masu tasowa, kazalika Sin tana goyon bayan kasashen duniya da su yi amfani da kimiyyar samar da allura kyauta, kuma tana goyon bayan WTO da sauran kungiyoyin kasa da kasa su yanke shawara a wannan fanni tun da wuri.”

Rashin daidaito game da samun allurar na kara tsananta a shekarar 2021, Xi Jinping ya yi kira da a yi watsi da tunanin kishin kasa a fannin samar da allurar don rarraba ta cikin daidaito da adalci. Kuma ya shawarci kasashen duniya da su kafa dandalin hadin kan kasa da kasa kan batun samar da allurar riga kafi.

Shawarar Xi Jinping ta samu amincewa daga bangarori daban-daban ciki hadda shugaban kungiyar IFRC, kana shugaban kungiyar Red Cross ta Italiya Francis Roca.

A ranar 12 ga watan Yuli, shirin kawance domin samar da allurar rigakafin cututuka na kasa da kasa wato GAVI ya sanar da kulla yarjejeniya da kamfanonin samar da allurar rigakafi na Sin guda biyu.  Bisa yarjejeniyar, wadannan kamfanonin biyu za su samarwa shirin COVAX allurai miliyan 110 kafin karshen watan Oktoba, daga baya kuma za su samar wa kasashe masu karanci ko matsakaicin kudin shiga allurai miliyan 500 ta hanyar COVAX.

Game da batun rarraba allura cikin daidaito da adalci, shugaba Xi Jinping ya ce, kamata ya yi mu nace wajen aiwatar da manufofi bisa kimiyya da hadin kan kasa da kasa don cika gibin da ake da shi a fannin samar da allura, tare da nuna adawa da siyasantar da batun cutar da dora laifi kan wani, ta yadda za a ingiza kafa kungiya ta bai daya ta kiwon lafiyar Bil Adama. (Amina Xu)

Not Found!(404)