Rahotannin daga kafafen yada labaran kasar Afirka ta Kudu sun ruwaito cewa, sabon ministan lafiyar kasar, Joe Phaahla ya sanar da cewa, kwamitin jagorantar ayyukan yaki da cutar COVID-19 na kasar ya riga ya amince da fara amfani da alluran riga-kafin da kamfanin Sinovac na kasar Sin ya samar, wajen kandagarkin yaduwar cutar.
Kwamitin jagorantar ayyukan yaki da cutar COVID-19, hukuma ce ta koli a bangaren tsara manufofin yaki da cutar a kasar Afirka ta Kudu. Tuni a ranar 3 ga watan Yulin bana, hukumar sa ido kan kayayyakin da suka shafi kiwon lafiya ta kasar ko kuma SAHPRA a takaice, ta sanar da fara amfani da alluran riga-kafin da kamfanin Sinovac ya samar cikin gaggawa kuma bisa wasu sharuddan da aka gindaya. (Murtala Zhang)