Wani kaso na alluran rigakafin kamfanin Sinopharm na kasar Sin, ya isa kasar Zambia a jiya Asabar.
Jirgin saman kamfanin Ethiopian na kasar Habasha dauke da alluran ya isa filin jirgin saman kasa da kasa na Kenneth Kaunda ne a jiya, inda jakadan Sin dake kasar Li Jie da babban sakataren dake kula da harkokin fasaha na ma’aikatar lafiya ta kasar Kennedy Malama, tare da wasu jami’an hukumomin MDD suka shaida isar rigakafin.
Jakadan kasar Sin ya ce gudunmuwar wata muhimmiyar alama ce ta kawance da hadin kai na hakika dake tsakanin gwamnatoci da jama’ar kasashen biyu wajen yaki da annobar.
Ya kara da cewa, yana fatan gudunmuwar rigakafin da alluran sirinji, za su taimakawa kokarin kasar Zambia na yaki da annobar, yana mai cewa hadin kai na da muhimmanci wajen yaki da annobar.
Jakadan na kasar Sin ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da rigakafin COVID-19 ya zama hajar da al’umma a ko ina za su iya samu, inda ya yi kira ga dukkan bangarori da su ci gaba da kokarin tabbatar da samar da shi kan farashi mai rahusa ga kasashe masu tasowa.
A nasa bangaren jami’in gwamnatin Zambia, ya godewa kasar Sin da wannan gudunmuwa, yana mai cewa za ta taimaka wajen karfafa shirin gwamnatin kasar Zambia na yi wa al’umma rigakafin.
Kennedy Malama ya kara da cewa, shirin kasar na yi wa al’umma rigakafi na bukatar karin taimako, bisa la’akari da cewa akwai mutane da dama da ba su karbi allurar ba. (Fa’iza Mustapha)