Annobar cutar COVID-19 ta kara yaduwa a sassan Afirka, saboda ba a yi wa al’ummomin nahiyar alluran rigakafi kamar yadda ake fata ba

CRI2021-08-06 13:46:31

Annobar cutar COVID-19 ta kara yaduwa a sassan Afirka, saboda ba a yi wa al’ummomin nahiyar alluran rigakafi kamar yadda ake fata ba_fororder_hoto

Ya zuwa yanzu, adadin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen duniya ya zarce miliyan 200, kuma bayanin da cibiyar rigakafi da dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka ta fidda a ranar 4 ga wata, ya nuna cewa, gaba daya, akwai mutanen nahiyar Afirka sama da miliyan 6.82 da suka kamu da cutar COVID-19, kana mutane sama da dubu 170 sun rasu sakamakon wannan cuta.

Kwanan baya, annobar cutar COVID-19 ta kara yaduwa a wasu sassan nahiyar Afirka, amma, ba a yiwa al’ummomin nahiyar alluran rigakafin cutar kamar yadda ake fata ba. Bayanin hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO ya nuna cewa, adadin wadanda aka yiwa alluran rigakafin COVID-19 a nahiyar Afirka, bai kai kashi 2 bisa dari ba na adadin wadanda aka yiwa alluran rigakafi a fadin duniya ba.

Dangane da wannan batu, ga Karin bayani daga Maryam…

Ya zuwa yanzu, kashi 1.5 bisa dari na al’ummar nahiyar Afirka ne, suka karbi alluran rigakafin cutar COVID-19. Masana na ganin cewa, akwai wasu dalilan da suka sa, ba a yi wa al’ummomin nahiyar Afirka alluran rigakafi kamar yadda ake fata ba. Da farko, shi ne, wasu al’ummar nahiyar ba su son karbar alluran rigakafin, a sa’i daya kuma, ana fama da matsalar karancin alluran rigakafi a wasu kasashen Afirka. Amma, alluran rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka, suna taimakawa kasashen wajen gaggauta aikin yi wa al’ummominsu alluran rigakafi.

Kasar Afirka ta Kudu ce kasar da ta fi fama da matsalar yaduwar wannan annoba a nahiyar Afirka, ya zuwa ranar 4 ga wata, gaba daya, akwai mutane sama da miliyan 2.48 da suka kamu da cutar COVID-19. A ranar 10 ga watan Yuni, annobar cutar COVID-19 ta barke a karo na uku a kasar Afirka ta Kudu, ko da yake kasar ta dauki matakan dakile yaduwar annoba, amma, hakan bai hana yaduwar cutar ba. Musamman ma a farkon watan Yuli, annobar cutar COVID-19 ta kara yaduwa a fadin kasar, sakamakon tashe-tashen hankulan da aka yi a kasar.

Sa’an nan, a ranar 25 ga watan Yuli, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta sanar da soke matakan kullen da ta sanya da sauransu, duk da cewa an wuce matsayin koli na yaduwar cutar COVID-19, amma, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin kasar, ya zarce dubu 10 a ko wace rana, kana, a ranar 4 ga watan nan da muke ciki, adadin ya kai sama da dubu 13.

A farkon watan Yuli, Hukumar kula da ingancin kayayyakin kiwon lafiya ta kasar Afirka ta Kudu, ta amince da yin amfani da alluran rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Sinovac na kasar Sin ya samar cikin gaggawa, lamarin da ya taimaka wajen gaggauta aikin yi wa al’ummomin kasar alluran rigakafi. A halin yanzu, mutane kimanin dubu 200 ne suke karbar alluran rigakafi a ko wace rana a kasar Afirka ta Kudu. Kuma, ya zuwa ranar 4 ga wata, gaba daya, mutane miliyan 3.32 sun karbi cikakkun alluran rigakafi a kasar Afirka ta Kudu, adadin da ya kai kashi 5.6 bisa dari na dukkan yawan al’ummar kasar.

Haka kuma, annobar cutar COVID-19 ta barke a zagaye na uku a kasar Botswana. Ya zuwa karshen watan Yuli, gaba daya, an tabbatar da mutane dubu 110 da suka kamu da cutar COVID-19. An kuma rufe dukkanin makarantu na kasar daga ranar 16 ga watan Yuli zuwa ranar 7 ga watan Agusta, domin dakile yaduwar wannan annoba.

Kwanan baya, kungiyar ma’aikatan nas-nas ta kasar Botswana, ta sanar da cewa, nas-nas dake aiki a asibitoci na kasar, suna fuskantar babbar matsala, sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar cikin sauri a kasar, da kuma karancin kayayyakin rigakafi. Bayanai na cewa, akwai nas-nas sama da dari 8 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar, kuma, 20 daga cikinsu sun rasu.

A halin yanzu kuma, kasar Botswana ce ke kan gaba wajen samun alluran rigakafin cutar COVID-19 daga kamfanin Sinovac na kasar Sin, kuma, mutane kimanin dubu 240 sun karbi alluran rigakafin a kasar, kana, mutane dubu 130 daga cikinsu, sun karbi cikakkun alluran rigakafi.

A kasar Uganda kuma, gwamnatin kasar tana dukufa wajen samar wa dukkanin al’ummomin kasar alluran rigakafi. Ya zuwa yanzu, ta sami alluran rigakafi miliyan 1.7, amma, kamar yadda sauran kasashen nahiyar Afirka suke, ba ta yi wa al’ummomin kasar alluran rigakafi kamar yadda take fata ba. Ya zuwa yanzu, an yi wa ‘yan kasar kimanin miliyan 1.14 alluran rigakafin, cikin al’ummar kasar da ta kai miliyan 43.

A ranar 31 ga watan Yuli ne, alluran rigakafin da kasar Sin ta samar wa kasar Uganda, suka isa kasar. Ministar harkokin kiwon lafiya ta kasar Jane Ruth Aceng ta bayyana cewa, alluran rigakafin da kasar Sin ta samar wa kasarta, sun taimaka matuka wajen biyan bukatun al’ummomin kasar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Not Found!(404)