Sudan na fatan cimma matsaya da ‘yan adawa

CRI2021-06-01 12:35:23

Gwamnatin rikon kwarya a Sudan, ta ce tana da karfin gwiwar cimma yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da bangaren babbar kungiyar ‘yan adawar kasar, wato Sudan People's Liberation Movement-North ko SPLM-N a takaice.

Babban mai shiga tsakani na gwamnatin rikon kwaryar Sudan, kuma ministan lura da ayyukan hukuma Khalid Omer Yousif ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Litinin, bayan tattaunawar da sassan biyu suka gudanar jiya a birnin Juba na Sudan ta Kudu. Yousif ya ce akwai alamun za a cimma matsaya da tsagin ‘yan adawar, dake karkashin jagorancin Abdel Aziz Al-Hilu.

Jami’in na Sudan, ya ce ko da yake suna da ta cewa game da wasu batutuwa da bangaren ‘yan adawar ya gabatar, amma duk da haka, za su ci gaba da shawarwari har zuwa matakin karshe, na cimma yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya.

A watan Oktoban bara, tsagin SPLM-N ya ki amincewa ya sanya hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da bangaren gwamnatin Sudan, da sauran sassa 5 na ‘yan adawar kasar masu dauke da makamai, a zaman da ya gudana a birnin Juba, bisa bukatar SPLM-N din na sai Sudan ta koma salon mulkin dimokaradiyya, mai kunshe da gwamnatin da ba ruwan ta da addini, wadda kuma za ta baiwa kowa damar bin addinin da ya zaba.  (Saminu)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)