Sudan ta Kudu ta rushe majalisar dokokin kasar bisa tanadin yarjejeniyar zaman lafiya ta kasar

CRI2021-05-10 09:54:50

Sudan ta Kudu ta rushe majalisar dokokin kasar bisa tanadin yarjejeniyar zaman lafiya ta kasar_fororder_s-sudan

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya sanar da rushe majalisar dokokin kasar, a matsayin wani bangare na farfado da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar da aka cimma a 2018.

Cikin wani umarnin shugaban kasa da aka watsa ta kafar talabijin da yammacin ranar Asabar, shugaba Kiir ya rushe majalisar dokokin kasar da majalisar jihohi , domin bada dama ga sake fasalin majalisun.

Sai dai, shugaban bai sanar da lokacin da sabbin majalisun za su fara aiki ba.

Kafa sabuwar majalisar dokoki wani bangare ne na yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu a watan Satumban 2018, tsakanin Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa na wancan lokaci wato Riek Machar.

Karkashin yarjejeniyar da aka farfado da ita, za a fadada sabuwar majalisar daga mai mambobi 400 zuwa 550, wadda za ta hada sabbin mambobin da suka fito daga dukkan bangarorin dake cikin yarjejeniyar ta 2018. (Fa’iza Mustapha)

Not Found!(404)