Kwanan nan, kashi na 16 na sojoji injiniyoyin wanzar da zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Sudan, sun yi nasarar samun amincewa daga tawaga ta musamman ta wanzar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya gami da kungiyar tarayyar Afirka AU suka tura cikin hadin-gwiwa zuwa yankin Darfur, a fannin binciken na’urori da makaman da suke da su, kafin a janye su daga wurin.
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta hadin-gwiwar Majalisar Dinkin Duniya gami da kungiyar tarayyar Afirka AU a yankin Darfur ta gudanar da binicke daga dukkanin fannoni kan na’urori da kayayyaki da yawa, ciki har da motoci, da na’urorin aikin gine-gine, da makamai da harsasai, da asibitocin da sassan rayuwar da aka gina.
Wani babban jami’in kula da aikin binciken ya bayyana cewa, sojoji injiniyoyin kasar Sin sun shirya tsaf don karbar binciken da aka yi musu, kuma sun samu amincewa dari bisa dari bisa ma’aunin MDD.
A watan Disambar bara, MDD gami da AU suka sanar da kammala ayyukan shimfida zaman lafiyar da tawagarsu ta kwashe tsawon shekaru 14 tana yi a kasar Sudan, kuma tun daga watan Janairun bana, membobin tawagar suka fara janyewa daga wurin. Sojojin kasar Sin su ma za su fara janyewa daga yankin Darfur na Sudan. (Murtala Zhang)