Babban jami’in hukumar agaji ta MDD a Sudan ta kudu ya yi Allah wadai da kashe wani ma’aikacin agaji a yankin Budi dake kasar.
Alain Noudehou, jami’in gudanarwar hukumar agaji ta MDD a Sudan ta kudu, ya ce an kashe ma’aikacin agajin ne a ranar Laraba lokacin da wasu bata gari suka bude wuta kan wata motar hukumar agajin yayin da take kan hanyarta zuwa wani asibiti.
Noudehou ya ce, motar tana daga cikin ayarin tawagar kungiyoyin agaji masu zaman kansu na kasa da kasa da na jami’an lafiyar gwamnatin kasar Sudan ta kudun.
Ya ce tawagar suna kan hanyarsu ne daga yankin Chukudum zuwa Kapoeta yankin da aka sha fuskantar hare-hare daga gefen tituna a wannan shekarar, kana ya bukaci gwamnati da ta kara yawan jami’an tsaro a kan wadannan hanyoyin.
Jami’in MDD ya bukaci hukumomi da al’umma da su tabbatar jami’an agajin suna iya samun damar tafiye-tafiye a kan hanyoyin da kuma raba kayan tallafin ga mutanen dake cikin tsananin bukatar agaji a kasar. (Ahmad)