Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta kudu (UNMISS), ya bayyana matukar damuwa dangane da ta’azzarar sabon rikici a yankin Greater Pibor dake gabashin kasar.
Nicholas Haysom, wakilin musamman na Sakatare Janar na MDD ya ce rikici tsakanin wasu kungiyoyi masu dauke da makamai, wanda ke kama da irin wanda aka gani a farkon bana, zai raba fararen hula da matsugunansu tare da barazana ga ayyukan agajin ceton rayuka na rabon abinci da ake yi a yankin.
Wata sanarwa da ya fitar a Juba ta ce kare al’umma, a duk inda suke daga rikici, shi ne babban hakkin da ya rataya a wuyan gwamnati da jami’anta na tsaro.
Ya ce ta’azzarar rikicin kwatsam, ya kai ga raba karin mutane da muhallansu da kuma dakatar da ayyukan agaji a Gumuruk da Verteth, inda ake raba abinci. Ya yi kira ga gwamnatin kasar ta kare maimaituwar rikicin, ta dauki mataki wajen magance tushensa da cika alkawarinta na kare fararen hula. (Fa’iza Mustapha)