WHO: Wasu ba su dauki matakai cikin lokaci kan yaki da annobar COVID-19 ba

CRI2021-03-11 15:44:19

A ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020, hukumar lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta sanar da cewa, barkewar annobar COVID-19 ta kasance kamar wani batun lafiyar al’umma na gaggawa da dole ne kasashen duniya su mai da hankali a kai. A ranar 8 ga watan nan da muka ciki, Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban darektan WHO ya bayyana wa manema labaru cewa, ya zama dole a kara gano dalilin da ya sa wasu kasashe suka dauki matakai, yayin da wasu ba su yi komai ba. Kana kuma Michael Ryan, darektan zartaswa mai kula da shirin gaggawa kan lafiyar al’umma na WHO ya bayyana ba tare da rufa-rufa ba cewa, kasashe da dama suna ganin cewa, ba ruwansu da barkewar annobar.(Tasallah Yuan)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)