Jami’in WHO: ba a bukatar “Fasfon Corona” amma ba lallai a kauce masa ba

CRI2021-03-05 10:55:23

Yayin da ake kara samun karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a nahiyar Turai, daraktan hukumar lafiya ta duniya a nahiyar, Hans Kluge, ya bukaci kasashen nahiyar su mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci yayin da suke tunkarar annobar.

Yayin wani taron manema labarai ta kafar bidiyo a jiya, Hans Kluge ya ce yayin da sabbin masu kamuwa da cutar a nahiyar suka karu da kaso 9 inda suka dara miliyan 1, adadin ya kawo karshen raguwar da aka samu cikin makonni shida da suka gaba, tare da bayyana yadda nau’o’in cutar ke kara kutsawa nahiyar

Sai dai, jami’in ya ki goyon bayan batun kirkiro “fasfon Corona” da galibin kasashen Turai ke nazari.

Da yake bayyana samar da fasfon na Corona a matsayin mai yuwuwa da za a iya bukata, Hans Kluge ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, batun ya zo da wasu sharudda

A cewarsa, abun da WHO ta fi damuwa da shi, shi ne samar da riga kafin da zai taikamaka wajen rage matsalar rashin daidaiton adadinsa a tsakanin kasashe. (Fa’iza Mustapha)

Not Found!(404)