A jiya ne, Ngozi Okonjo-Iweala, mace ta farko kuma ‘yar Afirka, ta fara aiki a matsayin babbar darektan kungiyar cinikayya ta duniya (WTO), abin da ya kawo karshen tsawon watanni shida da kungiyar ta shafe ba tare shugaba ba. Bayan da tsohon shugabanta Roberto Azevedo ya sauka daga mukamin a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2020, shekara guda kafin cikar wa’adinsa.
A jawabinta ga hukumar gudanarwar kungiyar a ranar farko ta kama aiki, Dr. Okonjo-Iweala ta yi alkawarin amfani da Ilimi da kwarewarta wajen jagorantar, abin da ta kira, daya daga cikin hukumomi masu muhimmanci a duniya.
Ta ce, duk da jan aikin dake gabansu, a shirye take wajen ganin an yiwa kungiyar gyaran fuska, har ma ta kai ga cimma nasarori. A ranar 15 ga watan Fabrairun wannan shekara ce, mambobin kungiyar baki daya, suka amince da nadin tsohuwar ministan kudin Najeriya, a matsayin sabuwar babbar darektar kungiyar. Kuma wa’adinta zai kare ne a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2025, koda yake tana iya neman sabuntawa.(Ibrahim)