WHO: Shirin yin rigakafin COVID-19 a Afrika ya matse kaimi

CRI2021-02-27 16:39:57

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce aikin kai rigakafin cutar COVID-19 nahiyar Afrika na tafiya cikin sauri, yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar da sake bude tattalin arzikin nahiyar.

Daraktar WHO a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce nahiyar ta matse kaimi wajen sayen rigakafin, domin yi wa wasu rukunonin dake fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

A ranar Laraba ne Ghana ta zama kasa ta farko a nahiyar da ta karbi alluran rigakafi 600,000 na kamfanin AstraZeneca, ta hannun shirin COVAX.

A cewar daraktar, Cote d’Ivoire za ta karbi nata kason a ranar Juma’a, yayin da ake sa ran kasashen Afrika 24, za su karbi na su kason karkashin shirin COVAX a cikin makwanni 2 masu zuwa.

Ta kara da cewa, galibin kasashen nahiyar sun shiga shirin kawancen kasashen duniya na samar da alluran rigakafin COVID-19 wato COVAX, kuma sun kafa ingantattun tsarukan saukaka yi wa jama’a masu yawa allurar rigakafin na COVID-19.(Fa’iza Mustapha)

Not Found!(404)