A jiya Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a wajen wani taron manema labaru cewa, ya kamata a gudanar da bincike kan cibiyar nazarin kwayoyin halittu ta Fort Detrick dake kasar Amurka.
A wajen taron, an yi wa Mista Zhao tambaya cewa, akwai wasu jami’an kasar Sin da suka yi kira domin a gudanar da bincike kan Fort Detrick, ko ana ganin cewa nazarin da ake yi kan wasu kwayoyin cututtuka ka iya zama barazana ga lafiyar jama’a? Kana ko ya kamata a kara kokarin sa ido kan wadannan dakunan gwaji dake kasashe daban daban?
Yayin amsa wadannan tambayoyi Zhao Lijian ya ce, ana fatan ganin wasu kasashe za su yi koyi da kasar Sin, wajen hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO, don neman ganin asalin cutar COVID-19. A wannan fanni kuma, kasar Sin ta riga ta ba hukumar WHO damar gudanar da bincike a cikin gidanta, don haka tana fatan sauran kasashe masu ruwa da tsaki su ma za su yarda da hakan. (Bello Wang)