30-Apr-2025
Dr. Sunday Isuwa, editan labarai ne a jaridar Leadership dake tarayyar Najeriya. Kwanan nan ya shigo kasar Sin, inda ya halarci horaswa da aka shirya musu, game da sirrin ci gaban kasar Sin a biranen Beijing da Chongqing. Mista Sunday Isuwa ya ce ci gaban kasar Sin ya wuce wasa, kuma bisa abun da ya ji ya gani a nan kasar, wasu rahotannin da aka ruwaito game da kasar Sin, ba daidai ba ne.
29-Apr-2025
A cikin birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, dalibar kasar Rasha Nastya tana karatu don neman digiri na biyu a fannin ilimin koyar da harshen Sin na kasa da kasa. Tana yin hakan ne domin kafa tushe mai karfi na zama malama wadda za ta karfafa mu’amalar al'adu tsakanin Rasha da Sin, tare da shimfida ire-iren abota a tsakanin al'ummomin kasashen biyu. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labari ne game da wata baiwar Allah mai suna Nastya, ’yar kasar Rasha dake karatu a nan kasar Sin.
28-Apr-2025