Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kotun tsarin mulkin Guinea ta tabbatar da nasarar Alpha Conde a zaben shugabancin kasar
2020-11-08 16:41:48        cri
Shugaban kasar Guinea mai ci Alpha Conde ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 18 ga watan Oktoba, kamar yadda shugaban kotun kundin tsarin mulkin kasar CC, Mohamed Lamine Bangoura, ya ayyana a ranar Asabar a jawabin da ya gabatarwa al'ummar kasar.

A cewar shugaban na CC, Alpha Conde, dan takarar jam'iyya mai mulki ta RPG, ya yi nasarar lashe zaben da kashi 59.50 na yawan kuri'un da aka kada, inda ya yi galaba kan babban abokin karawarsa na jam'iyyar adawa Cellou Dalein Diallo, wanda ya samu kashi 33.49 bisa 100 da yawan kuri'un.

Shugaban kotun ta CC ya ce, kuri'un da aka kada a zaben na ranar 18 ga watan Oktoba an kidaya su yadda ya kamata kuma shugaban kasar mai ci Alpha Conde shi ne ya lashe zaben shugabancin kasar Guinea.

An kiyasta kashi 78.88 bisa 100 na yawan mutanen kasar ne suka fita zaben shugaban kasar, inda 'yan takara 12 suka fafata a zaben na ranar 18 ga watan Oktoba. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China