Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakiliyar MDD ta bukaci kasa da kasa su cigaba da daukar matakan kan batun Guinea-Bissau
2020-08-11 12:00:48        cri
Babbar wakiliyar MDD a Guinea-Bissau ta jaddada bukatar kasa da kasa su ci gaba da taka rawarsu kan batun kasar Guinea-Bissau yayin da ake sa ran kawo karshen shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar nan da karshen wannan shekara.

Rosine Sori-Coulibaly, wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD kuma shugabar ofishin shirin MDD na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a Guinea-Bissau(UNIOGBIS), tace, cigaban siyasa da aka samu na baya bayan nan a kasar ya haifar da sauyawar halin siyasar kasar, lamarin da ya sa aka samu karin rashin yarda da juna a tsakanin masu ruwa da tsaki. Yawan zarge zarge, da rahotannin cin zarafi da muzgunawar da ake nunawa masu adawa da sabon tsarin siyasar kasar, ya haifar da rudanin siyasa a kasar, lamarin da ya sa aka kai matakin rashin cimma matsayar warware takaddamar siyasar kasar da kuma gaza gina tsarin zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Rosine ta bayyanawa kwamitin sulhun MDD cewa, hasashen da aka yi game da a halin da ake ciki a yanzu da kuma nan gaba ya tilasta bukatar cigaba da daukar kwararan matakai daga bangarorin kasa da kasa domin kaucewa tabarbarewar yanayin siyasa da yanayin kare hakkin dan adam a kasar, da kokarin tabbatar da nasarorin siyasar da aka samu a lokutan baya, kana da kiyaye matakan da zasu wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China