Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Sin sun bada gudunmawar na'urorin taimakon numfashi ga kasar Guinea-Bissau
2020-06-13 16:04:00        cri
Kamfanonin kasar Sin 4 dake kasar Guinea-Bissau sun bada gudunmuwar na'urorin taimakon numfashi 2, ga hukumomin lafiya na kasar, domin taimaka musu jinyar masu cutar COVID-19.

Yayin bikin mika gudunmawar, Jakadan kasar Sin a Guinea-Bissa, Jin Hongjun, ya nanata kudurin gwamnatin kasar Sin na ci gaba da tallafawa al'ummar Guinea-Bissau a yakin da suke da COVID-19.

Jakadan ya kara da cewa, a mako mai zuwa, wani karin gudunmawar kayayyakin lafiya daga gwamnatin kasar Sin za ta isa Guinea-Bissau. Yana mai cewa, gudunmawar dake tafe, za ta taimaka wajen inganta yanayin aiki ga jami'an lafiya.

Bugu da kari, ya ce goyon bayan juna na da muhimmanci gaya wajen fatattakar cutar, wadda ta zama abokiyar gabar bil adama. Yana mai cewa, gudunmawar da kamfanonin kasar Sin suka bayar, alamu ne na goyon baya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China