Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren MDD ya bukaci a kwantar da hankula da Guinea
2020-10-25 16:27:06        cri
A jiya Asabar, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci a zauna lafiya a kasar Guinea bayan da aka sanar da sakamakon farko na zaben shugaban kasar.

Sanarwar da Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDDr ya fitar ta ce, babban sakataren ya yi kiran ne bayan sanarwar da hukumar zaben kasar ta fidda. Ya jaddada kiran nasa ga dukkan bangarorin siyasar kasar dasu warware duk wata takaddama ta hanyar daukar matakan shara'a, kana su guji tada hankali.

Guterres, yayi Allah wadai da babbar murya game da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar, musamman, tsakanin bangaren shugaban kasar Guinea da madugun 'yan adawar kasar, inda ya bukace su da su ja kunnen magoya bayansu dasu gaggauta dakatar da tashin hankali kuma su amince da shiga tattaunawar sulhu domin lalibo hanyar wanzar da zaman lafiyar rikicin da ya barke na bayan zaben kasar.

Babban sakataren MDD ya kuma bukaci masu fada a ji da kafafen yada labarai da su kaucewa duk wasu hanyoyin da zasu kara ruruta wutar rikicin da ake danganta shi da kabilanci a kasar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China