Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 22
2020-11-06 12:32:01        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 22, bayan da sojojin kasa suka dakile wasu hare-haren da mayakan suka kai, a kan sansanin sojojin a 'yan kwanakin da suka gabata a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun sojojin John Enechen, ya bayyana jiya Alhamis cewa, sojojin sun cimma wannan nasara ce, bisa goyon baya gami da luguden wuta daga sojojin sama, wani bangare na shirin yaki da mayakan na Boko Haram mai suna Operation Lafiya Dole da ake ci gaba da aiwatarwa a yankin.

Da yake Karin haske game da hare-haren da sojojin ke kaddamarwa a yankin na arewa maso gabas da ma sauran sassan kasar daga ranakun Juma'a zuwa Larabar da suka gabata kuwa, Enechen ya ce, dakarun sun yi nasarar dakile hare-haren da 'yan ta'addan suka kaddamar a kan lokaci. Sai dai bai bayyana takamamman lokaci ba. Haka kuma sojojin sun yi nasasar kwato tarin makamai da albarusai da na'urori a lokacin bata kashin.

A cewarsa, sojojin tare da hadin gwiwar 'yan banga a yankin, sun yi nasarar kama wani dan kungiyar ta Boko Haram a garin Damaturu, babban birnin jijhar Yobe dake yankin arewa maso gabashin kasar, yayin da yake kokarin sayan makamai da albarusai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China