Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta gina karin filayen jiragen sama 10
2020-10-29 10:52:02        cri
Ministan sufurin jiragen sama a tarayyar Najeriya Hadi Sirika, ya ce gwamnatin kasar za ta gina sabbin filayen jiragen sama 10 a sassan kasar daban daban, a wani mataki na bunkasa harkokin sufurin jiragen sama a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Cikin wata sanarwa da ofishin ministan ya fitar a jiya Laraba, wadda kuma kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, Hadi Sirika ya ce, hakan daya ne daga ginshikan ciyar da kasar gaba a fannin sufurin jiragen sama, karkashin wani shiri da mahukuntan kasar suka kaddamar a shekarar 2015, wanda kuma ake aiwatarwa har yanzu.

Hadi Sirika ya kara da cewa, sabbin filayen jiragen da ake fatan ginawa, za su kai kusan rabin wadanda kasar ke da su a yanzu. Gabanin hakan, yayin da yake kare kasafin kudin ma'aikatar sa na shekarar 2021 a ranar Talata, ministan ya shaidawa kwamitin majalissar dokokin kasar mai kula da sufurin sama cewa, fannin sufurin saman Najeriya ya samu ci gaba, ciki hadda karuwar yawan filayen jiragen sama, tun bayan kaddamar da shirin raya shi cikin shekaru 5 da suka gabata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China