Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gabatar da Okonjo-Iweala daga Najeriya don zama sabuwar shugabar WTO amma Amurka ta nuna adawa
2020-10-29 09:37:53        cri

Tsohuwar ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala an gabatar da ita don zama sabuwar babbar daraktar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO, kamar yadda jami'in WTO ya sanar a jiya Laraba.

Kakakin hukumar ta WTO, Keith Rockwell, ya fadawa taron manema labarai cewa, manyan jakadu uku na WTO, da ake kira "troika," sun gabatar da sunan Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugaban kungiyar mai helkwata a Geneva a lokacin wani taron ganawar sirri da suka gudanar, sun yake shawarar cewa 'yar takarar ta samu amincewar mambobin.

Sai dai kuma, akwai wakili daya tilo da bai goyi bayan takarar ta Dr. Ngozi ba, Rockwell ya ce Amurka ce bata goyi bayan takarar ba, ta nuna cewar za ta goyi bayan ministar Koriya ta kudu Yoo.

Ana sa ran za a amince da takarar Okonjo-Iweala a lokacin babban taron WTO a ranar 9 ga watan Nuwamba, idan an amince, zata zamanto mace ta farko da zata jagoranci kungiyar WTO.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China