Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 22
2020-10-30 09:56:44        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarun ta sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram 22, yayin wani dauki ba dadi da suka yi da 'yan ta'addan a baya bayan nan, a gabar da sojojin ke ta daukar matakan kakkabe gyauron 'yan Boko Haram, daga yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Alhamis, kakakin rundunar Benard Onyeuko, ya ce sojojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda a ranar 25 ga watan Oktobar nan, a garin Damboa dake jihar Borno, bayan da 'yan ta'addan suka yi yunkurin murkushe sansanin sojoji dake garin.

Benard Onyeuko, ya ce 'yan ta'addan sun gamu da gamon su, duba da yadda sojojin suka yi musu ruwan wuta ta kasa, yayin da wasu jiragen saman yaki na sojin kasar ma suka rika kaiwa mayakan na Boko Haram hare hare ta sama.

Jami'in ya kara da cewa, da yawa daga mayakan sun tsere da harbin bindiga a jikin su, an kuma lalata wasu motoci 2 masu dake da bindigogi da mayakan ke amfani da su yayin artabun.

To sai dai kuma ya ce wasu daga dakarun sojin kasar ma sun samu raunuka, duk da dai bai fayyace adadin su ba. Sai dai ya ce an kwashe su daga sansanin sojin zuwa cibiyar kula da lafiya ta dakarun. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China