Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga 5 a arewacin Najeriya
2020-10-29 09:49:36        cri
'Yan sanda a Najeriya sun tabbatar da kisan 'yan bindiga 5 a wani samame da jami'an tsaron kasar suka kaddamar wanda ya hada har da sojoji, inda suka kaddamar da harin kan 'yan bindigar a jahar Katsina dake arewa maso yammacin kasar.

'Yan bindigar sun kashe farar hula guda a lokacin musayar wuta da aka yi a ranar Talata a yankin Tsaskiya dake karamar hukumar Safana a jahar, kakakin rundunar 'yan sandan jahar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin.

An gano wasu mata uku dake boye a cikin dajin a lokacin harin, wadanda 'yan bindigar suka yi garkuwa da su, inji kakakin 'yan sandan.

Gambo Isah ya ce, 'yan bindigar da yawansu ya zarce 200 dauke da muggan makamai, sun yiwa kauyen kawanya, sa'an nan sun kaddamar da hari ta hanyoyi uku da ake iya shiga kauyen.

Da dama daga cikin 'yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga bayan da jami'an tsaron suka afka musu, inji jami'in, ya kara da cewa, wasu jami'an tsaron sun bazama cikin dajin domin ceto matan da aka yi garkuwa dasu da kuma cafke 'yan bindigar da suka tsere da raunuka a jikinsu.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China