Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sako malamai 11 da aka yi garkuwa da su a yankin masu Magana da Turancin Ingilishi na Kamaru
2020-11-06 11:11:07        cri
Wasu malaman makaranta 11 da aka yi garkuwa da su a ranar Talata a yankin masu Magana da yaren Turancin Ingilishi a shiyyar arewa maso yammacin Kamaru sun kubuta da yammacin ranar Alhamis, kamar yadda hukumomi a kasar suka tabbatar.

Dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su malamai ne a makarantar firamare ta Presbyterian dake garin Kumbo, kuma an sako su ne bayan wata tattaunawa mai zurfi da aka gudanar da mayakan 'yan awaren da suka yi garkuwa da su, hukumar makarantar ta tabbatar da hakan.

Mayakan 'yan awaren sun afkawa makarantar ne inda suka yi awon gaba da malaman da kuma wasu ma'aikatan hukumar gudanarwar makarantar a ranar Talata a lokacin da dalibai ke ci gaba da daukar darrusa. Wasu yara dalibai da aka yi garkuwa da su tare da ma'aikatan makarantar an riga an sake su ba tare da bata lokaci ba bayan matsin lamba daga al'ummomin yankin, a cewar jami'an gwamnatin kasar.

An jima da bude makarantu a mafi yawan yankunan dake magana da yaren Faransanci a Kamaru a watan Oktoba, amma wasu mayakan 'yan awaren sun sha yin barazana ta kafafen yada labarai na zamani cewa zasu gurgunta harkokin karatu a kasar. Sun yi ikirarin cewa hanyar cikakkiyar tattaunawa da tsakaita bude wuta ne kadai zai tabbatar da samun nasarar bude makarantu a yankuna biyu na kasar masu magana da yaren Turancin Ingilishi dake shiyyoyin arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar, inda mayakan suka jima suna arangama tsakaninsu da dakarun gwamnati tun a shekarar 2017 inda suke fafutukar neman ballewa don kafa kasar Ambazonia.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China