Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya damu matuka game da harin da aka kaiwa makaranta a Kamaru
2020-10-26 10:40:08        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwa game da mummunan harin da aka kaddamar a ranar Asabar kan makaranta a garin Kumba dake shiyyar kudu maso yammacin Jamhuriyar Kamaru, inda aka bada rahoton yara masu yawa sun mutu kana wasu da dama sun samu raunuka.

Sanarwar da kakakin sakataren MDD Stephane Dujarric ya fitar ta ce, harin wani babban abin tada hankali ne dake karuwa kan fararen hula, wanda ya hada har da yara kanana, mafi yawa daga cikinsu an hana 'yancinsu na samun ilmi. Hare haren da ake kaiwa makarantu babban laifi ne dake tauye hakkin yara.

Babban sakataren ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan yaran da harin ya rutsa da su, kana ya yi fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka ji raunuka. Ya bukaci hukumomin kasar Kamaru su gudanar da cikakken bincike domin hukunta wadanda ke da alhakin daukar nauyin harin. Ya yi kira ga dukkan bangarorin masu dauke da makamai da su guji kaddamar da hare haren kan fararen hula kuma su mutunta hakkokin dan adam na kasa da kasa da kuma dokokin kare hakkin dan adam na kasa da kasa.

Babban sakaren ya yi kira da babbar murya ga dukkan bangarori da su amsa kiransa, su amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kasa da kasa. Ya jaddada aniyar MDD na shirya muhimmiyar tattaunawar lalubo bakin zaren warware matsalar tashin hankalin dake addabar yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China