Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD tayi Allah wadai da kashe yara 'yan makaranta a yankin masu magana da Turanci a Kamaru
2020-10-25 16:39:45        cri
Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD OCHA, ya yi Allah wadai da kisan yara 'yan makaranta a jamhuriyar Kamaru a yankin masu magana da yaren Turanci dake shiyyar kudu maso yammacin kasar.

Matthias Naab, jami'in shirin ayyukan jin kan bil adama dake Kamaru ya bayyana cikin wata sanarwa a Yaounde babban birnin kasar cewa, kaddamar da hari kan yara 'yan makaranta ba abin da za a laminta ba ne, kuma harin tamkar laifi ne na cin zarafin dan adam karkashin dokokin shara'a.

Da safiyar ranar Asabar ne, yayin da dalibai ke daukar darasi a aji a makarantar Mother Francisca International Bilingual Academy dake Kumba, a shiyyar kudu maso yammacin kasar, wasu 'yan bindiga suka afka musu inda suka bude musu wuta da harbe harbe. A cewar ofishin MDDr OCHA, an kashe a kalla yara 8 da kuma jikkata wasu 12.

Hukumomin yankin sun ce, an yi amanna maharan mayakan 'yan aware ne, wadanda ke kaddamar da hare hare a shiyyar tun a shekarar 2017.

Da ma dai mayakan 'yan awaren sun jima suna yaki da dakarun gwamnatin kasar tun a shekarar 2017 a yunkurinsu na neman ballewa don kafa kasa mai cin gashin kanta a shiyyoyin kasar biyu masu Magana da yaren Turanci, wato yankin arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China