Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwar sojojin Kamaru da Najeriya yana gudana cikin lumana
2020-10-22 16:31:13        cri
Wani babban jami'in sojojin Najeriya yace hadin gwiwar sojojin Kamaru da Najeriya yana kara kyautatuwa cikin lumana, kuma bisa yanayi mafi dacewa.

Janar Olufemi Odeyinde, na kwalejin horar da sojojin saman Najeriya ya bayyana hakan a lokacin wata ziyarar musayar jami'an sojojin Najeriya zuwa kwalejin horas da sojoji na kasa da kasa na Kamaru.

Jami'in ya bayyana cewa, sojojin Kamaru da na Najeriya suna yin musaya a tsakaninsu, da samun horo tare, kana suna yin hadin gwiwa ta kut-da-kut wajen yaki da ayyukan ta'addanci, da yakar 'yan aware da masu tsattsauran ra'ayi.

Ya ce hadin gwiwar yana biyan muradun bangarorin kasashen biyu, musamman bukatun wanzar da tsaro, da zaman lafiya, da cigaban shiyyoyin yammaci da tsakiyar Afrika.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China