Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta sanar da komawar harkokin wasanni a kasar
2020-10-02 16:51:40        cri
Ministan wasanni a kasar Kamaru, Narcisse Mouelle Kombi, ya sanar da komawar dukkan harkokin wasanni da na motsa jiki a kasar, bayan sun shafe watanni suna fuskantar tsaiko saboda annobar COVID-19.

Cikin wata sanarwar da ya fitar jiya, Ministan ya ce dole ne dukkan harkokin su gudana karkashin matakan kiwon lafiya da na yaki da COVID-19, kamar yadda gwamnati ta tanada.

Tun cikin watan Maris aka dakatar da dukkannin wasanni a kasar, bayan gwamnati ta hana gudanar da taruka saboda annobar COVID-19.

Ministan ya ce, komawar harkokin wasannin zai ba kasar damar matse kaimi wajen horo, yayin da take shirin karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2022 da kuma ta zakarun kasashen nahiyar ta 2021. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China