2020-11-02 10:48:43 cri |
Kasenmujiang Heilili wanda yake tafiyar da wani kamfanin kimiyar manhajoji a birnin Hotan dake jihar Xinjiang, ya taba samun horo a cibiyar koyon ilmin sana'o'i ta jihar. Ya waiwayi rayuwarsa kafin ya shiga cibiyar a wancan lokaci yana mai cewa, tsattsauran ra'ayi ya yi masa illa matuka, a tunaninsa, dole ne musulmai su yi nesa da duk abubuwan dake da alaka da Kafirci, idan ba haka ba, ba zai shiga Aljanna ba bayan ya mutu.
Karkashin wannan tunani, sannu a hankali Kasenmujiang Heilili ya yi nesa da abokansa, saboda a ganinsa abubuwan da suke yi ba su dace da musulunci ba, har ya zama mai tsattsauran ra'ayin, inda ya kan soki abokansa dake da alaka da Karfici. Mahaifansa sun yi bakin ciki matuka, inda suka gabatar masa wannan cibiya, da fatan ya samu horo a ciki.
Kasenmujiang Heilili ya ce, wannan cibiya wata nagartacciyar makaranta ce, inda ake samar da abinci da gidajen kwana, har da dukkanin abubuwan bukata na yau da kullum da na karatu a kyauta. Ban da wannan kuma, ana iya koyon daidaitaccen Sinanci da ilmin shari'a da doka da sana'o'i, don kawar da tsattsauran ra'ayi, sannan ana iya zuwa gida sau daya a kowanne mako. Yana mai cewa, irin wannan rayuwa ta yi kama da ta jami'a.
Bayan Kasenmujiang Heilili ya kammala horo ya koma gida, daidaitaccen Sinanci da ma fasahar sarrafa kamfani da ya koya a cibiyar sun taimaka masa wajen gudanar da kamfaninsa. Ban da wannan kuma, gwamnatin jihar ta ba shi shawarar samun rancen kudi daga banki bayan ya bayyana mata fatansa na habaka kamfaninsa. Yanzu gwamnatin ta taimaka masa wajen samun rancen kudi na RMB Yuan dubu 300. Kasenmujiang Heilili ya yi farin ciki matuka inda ya ce, "iyalina sun kara samun kwarin gwiwa ga rayuwata, kuma zan yi aure da budurwata, ina jin dadin zaman rayuwata ta yanzu matuka."(Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China