Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya bukaci a raya jihar Xinjiang don ta zama sabon wurin bude kofa ga kasashen waje
2020-09-27 16:50:28        cri

Jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, tana makwabtaka da wasu kasashe 8, ciki har da Rasha, da Kazakhstan, da Pakistan, da Mongoliya, da Indiya da dai sauransu. Bayan da ya ziyarci jihar a shekara ta 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira taro, inda ya bukaci a rubanya kokarin raya jihar don ta zama wani muhimmin yankin tattalin arziki dake kan "hanyar siliki".

Tun daga shekara ta 2014 zuwa yanzu, gwamnatin Xinjiang tana himmatuwa wajen raya wurin har ya zama muhimmiyar cibiyar zirga-zirga, da cudanyar kayayyaki, da hidimomin hada-hadar kudi, da kuma raya al'adu da kimiyya da fasaha, gami da cibiyar samar da hidimomin aikin jinya. Ya zuwa shekarar 2019, Xinjiang ta kaddamar da wasu hanyoyin surufin kayayyaki 111 da kasashe 5 dake makwabtaka da ita, har ma ta kaddamar da wasu layukan sadarwa 17 da kasashen Pakistan da Kazakhstan, al'amarin da ya kara dankon mu'amala da cudanya a tsakanin Xinjiang da kasashe makwabtanta.

A cikin shekaru 10 da suka shude, sau uku gwamnatin kasar Sin tana kiran taron sanin makamar aiki kan Xinjiang, inda aka tsara muradun raya yankin gami da wasu hanyoyin da suka dace wajen aiwatar da manufofin, kuma al'amarin da ya taimaka sosai wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a jihar ta Xinjiang.

A wajen taron sanin makamar aiki kan Xinjiang da gwamnatin kasar Sin ta shirya karo na biyu a shekara ta 2014, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, dangane da batun raya kudancin jihar, ya dace a aiwatar da wasu manufofin musamman da kawar da tsoffin ra'ayoyi. Kana, a wajen taron bana, ya sake jaddada cewa, ya zama dole a kara raya tattalin arziki gami da kyautata zaman rayuwar mazauna yankin kudancin jihar. Kuma ta hanyar daukar wasu matakan tallafawa matalauta, ciki har da sake tsugunar da mutane, da raya sana'o'i, daga shekara ta 2014 zuwa ta 2019, gaba daya akwai mutane kusan miliyan 1.9 wadanda suka fita daga kangin talauci a wasu yankuna hudu dake kudancin Xinjiang.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China