Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An cimma nasarar gudanarwar taron bunkasa zamantakewar al'umma da kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta Sin
2020-09-25 20:06:04        cri
A jiya Alhamis ne aka cimma nasarar gudanarwar taro mai nasaba da bunkasa zamantakewar al'umma, da kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kafar bidiyo.

Kwararrun daga jami'ar Xinjiang, da jami'ar koyon dokokin shari'a ta kudu maso yamma ta kasar Sin, sun yi tattaunawa mai zurfi kan babban taken taro, inda suka cimma ra'ayi daya cewa, an cimma sakamako da dama a fannin raya zamantakewar al'umma, da kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin, lamarin da ya karyata zargin da wasu 'yan siyasan yammacin kasashen duniya suke yiwa kasar Sin game da wannan batu.

Ofishin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD a birnin Geneva, da tawagar wakilan sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, da cibiyar nazarin harkokin hakkin dan Adam ta kasar Sin, da jami'ar koyon dokokin shari'a ta kudu maso yamma ta kasar Sin ne suka shirya wannan taro cikin hadin gwiwa. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China