Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kira taro mai nasaba da kawar da talauci da kare hakkin bil Adama
2020-09-25 20:06:46        cri
A ranar 21 ga wata, an kira taro mai nasaba da kawar da talauci da kare hakkin bil Adama ta kafar bidiyo. Kwararrun kasar Sin da na kasashen ketare sun yi bayani game da fasahohin kasar Sin na kawar da talauci, inda suka nuna amincewa kan babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar, a fannin kare hakkin bil Adama tsakanin kasa da kasa, ta hanyar kawar da talauci a kasar Sin.

Ofishin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD na birnin Geneva, da tawagar wakilan sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, da cibiyar nazarin harkokin hakkin dan Adam ta kasar Sin, da jami'ar Jinan ne suka shirya taron cikin hadin gwiwa. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China