Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xinjiang: Abu ne mawuyaci a samu bazuwar cutar COVID-19
2020-10-29 11:16:30        cri

 

Hukumar kula da lafiyar al'umma a jihar Xinjiang ta kasar Sin, ta wallafa a shafin ta na yanar gizo cewa, abu ne mawuyaci a samu bazuwar cutar numfashi ta COVID-19 a jihar, duba da yadda aka gaggauta yiwa al'ummun jihar, ciki hadda ma'aikatan kamfanin gine gine na Xinjiang gwayin kwayar cutar.

Hukumar ta ce an riga an tantance sabbin mutum 23 da suka harbu da cutar a ranar Laraba 28 ga watan nan, wadanda dukkanin su ba su nuna alamun kamuwa da ita ba, kuma suna zaune ne a gundumar Shufu ta yankin Kashgar. Kaza lika ba a samu karuwar irin wannan rukuni ba a halin yanzu.

A wani ci gaban kuma, da yammacin jiya Larabar, mataimakin darakta a cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka na yankin Kashgar Wang Xijiang, ya ce mahukuntan yankin sun shafe tsawon kwana 3 da yini 3, suna gudanar da ayyukan gwajin kwayar cutar a Kashgar, kuma ya zuwa karfe 5 na yammacin ranar Talata, inda ban da mutum 183 da ake da rahoton sun harbu da cutar a gundumar Shufu, dukkanin sauran mutanen da aka yi wa gwajin ba sa dauke da cutar, don haka zai yi wuya wannan cuta ta ci gaba da kara bazuwa a yanzu.

Wang Xijiang ya kara da cewa, gano mutane masu yawa dake dauke da cutar amma ba su nuna alamun ta ba a gundumar Shufu, na da nasaba da yadda aka gaggauta yiwa al'ummun yankin gwaji. Jami'in ya ce, yiwa wannan rukuni na mutane gwaji kan lokaci, ta samar da damar hanzarta daukar matakai, musamman a fannin jinya da kula da su har su warke. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China