Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Kasashen Afirka sun yaki COVID-19 yadda ya kamata ta yadda saurin karuwar alkaluman cutar ke kara raguwa
2020-10-26 11:27:18        cri

 

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Mr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce saurin karuwar adadin masu harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar Afirka na raguwa, kuma akwai kyakkyawan fatan cin lagon cutar.

Shi ma jagoran hukumar a nahiyar ta Afirka Matshidiso Moeti, ya ce alkaluman yaduwar cutar a nahiyar Afirka bai yi matukar karuwa ba, sabanin yadda a baya aka yi ta nuna damuwa game da yiwuwar hakan.

Sakamakon bincike ya nuna cewa, matakan da kasashen nahiyar suka dauka na gano masu dauke da cutar cikin sauri, da matakan kandagarki, da na jinyar masu dauke da ita, sun taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar yaki da ita.

Jami'in ya ce a watan Fabarairun wannan shekara ta bana, dakunan gwajin cutar guda 2 ne kacal a Afirka ta kudu da Senegal, amma kawo yanzu, akwai dakunan gwajin cutar sama da 750 a sassan nahiyar daban daban, ciki har da 12 da suka kai matsayin inganci da WHO ta gindaya. Kaza lika ya zuwa yanzu, an yiwa al'ummun nahiyar sama da miliyan 15 gwajin cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China