Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO na kira da a bunkasa ayyukan gwaji domin inganta yaki da COVID-19 a Afrika
2020-10-23 11:06:52        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bukaci kasashen Afrika su gaggauta rungumar gwaji domin bunkasa yaki da suke da COVID-19 a nahiyar.

Daraktan hukumar a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce karfin nahiyar na rage tasirin cutar kan zaman takewa da kayayyakin lafiya ya dogara ne da kara yawan gwaji a tsakanin mutane mafi fuskantar barazanar cutar.

A cewar sanarwar da ta fitar jiya, kara gwaji mai inganci zai bunkasa yadda nahiyar ke tunkarar cutar.

Ta ce WHO na bada shawarar gwajin kwayoyin garkuwar jiki, wanda zai iya sauya yadda nahiyar Afrika ke tunkarar annobar yayin da adadin wandada ke harbuwa da ita ke karuwa.

Kasashen Afrika da dama na fama da matsalar gwajin cutar COVID-19, wanda ke da alaka da karancin kayayyakin gwajin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China