Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalibai da malamai 181 sun kamu da COVID-19 a wata makaranta a Nijeriya
2020-10-17 16:09:36        cri

Jimilar dalibai da malamai 181 na wata makarantar sakandare mai zaman kanta dake jihar Lagos ta Nijeriya ne aka bayyana sun kamu da cutar COVID-19.

Kwamshinan lafiya na jihar, Akin Abayomi, ya ce an gano lamarin ne biyo bayan bibiyar da bincike a makarantar dake yankin Lekki na birnin Lagos.

Sai dai, kwamishinan ya ce daliban da malaman ba su nuna alamomin cutar ba.

Tun cikin watan Maris aka rufe makarantu a Nijeriya saboda barkewar annobar. sai dai a makonnin da suka gabata, hukumomi sun ba da umarnin sake bude su domin daliban dake ajujuwan karshe dake shirin rubuta jararrabawa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China