Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 1.7
2020-10-26 10:06:49        cri

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afrika, ta ce yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar ya kai 1,707,741.

Wata sanarwa da cibiyar ta fitar, ta ce yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu, ya kai 41,145, zuwa jiya Lahadi.

Ta ce kasashen da aka fi samun yawan masu cutar a nahiyar sun hada da Afrika ta kudu, da Masar, da Morocco, da Habasha, da Nijeriya.

Har ila yau, ta ce cutar ta fi kamari a yankin kudancin nahiyar, bisa la'akari da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da na wadanda cutar ta yi ajalinsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China