Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bukaci kasashen Afirka su kare tsoffi yayin da ake fama da COVID-19
2020-10-02 15:38:02        cri

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira da kasashen nahiyar Afirka, da su ba da muhimmanci ga lafiyar tsoffi, wadanda ke cikin hadarin kamuwa da annobar COVID-19, idan aka kwatanta da sauran rukunin al'umma.

Darektar hukumar mai kula da shiyyar Afirka Matshidiso Moeti, ita ce ta bayyana haka, tana mai cewa, tsoffi sun fi saurin kamuwa da cututtuka da ma mutuwa daga wannan annoba, a don haka ya kamata a dauki matakan da suka dace na ganin tsoffin ba su kamu da wannan cuta mai saurin kisa ba.

Wata sanarwa da jami'ar hukumar ta fitar, ta ce, sama da mutane 17,000 masu shekara sama da 55 sun mutu sakamakon COVID-19, adadin da ya kai sama da kaso 50 cikin 100 na wadanda cutar ta halaka a shiyyar. Muddin ana son magance yadda cutar ke shafar tsoffin mutane, Moeti ta ce wajibi ne shiyyar Afirka, ta dauki matakan kula da su, ciki har da amfani da matakan kandagarki na sanya kyallen rufe baki da hanci, da bayar da tazara, da wanke hannu akai-akai

Hukumar WHO ta ce, tana aiki da kasashen Afirka 40 wajen gina hadadden tsarin kula da tsoffi, matakin da ya mayar da hankali kan kula da lafiyar al'umma, da gano wadanda suka kamu da cutar a kan lokaci, da magance matsalar lafiya da kwakwalwa da taimakawa masu kula da tsoffi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China