Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afirka ta zarce miliyan 1.5
2020-10-05 16:43:37        cri
Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana cewa, yawan mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin nahiyar ya zuwa jiya Lahadi, ya kai 1,506,185, kana yawan wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya zuwa jiyan, ya kai mutane 36,614.

Haka kuma cibiyar ta bayyana cewa, yawan mutanen da suka warke daga cutar a sassan nahiyar ya kai 1,243,259.

A sakamakon mabanbantan tasirin da cutar take ci gaba da haifarwa a kasashen Afirka, cibiyar ta Africa CDC, ta ce kasashen da cutar ta fi harba a kasashen Afirka, sun hada da Afirka ta kudu, da Morocco, da Masar da Habasha, da kuma Najeriya.

Haka kuma cibiyar ta ce, akwai kasashe 12 na Afirka dake da kaso 3 cikin 100 na yawan mutanen da cutar ta halaka a duniya. Kasashen sun hada da Chadi, da Liberia, da Nijar da Mali da Angola, da Aljeriya da kuma Sudan. Kana matsakaicin yawan wadanda cutar ta halaka a nahiyar a halin yanzu, ya kai kimanin kaso 2.4 cikin 100.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China