Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya kai miliyan 1.47
2020-10-01 16:58:21        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a Afrika ya kai 1,472,433 ya zuwa ranar Laraba.

A rahoton da Afrika CDC ta fitar na baya bayan nan ta ce, ya zuwa ranar Laraba, an gudanar da gwaje gwajen annobar COVID-19 sama da miliyan 14.8 a duk fadin nahiyar ta Afrika inda aka samu kashi 10 bisa 100 na sakamakon gwajin sun kamu da cutar ta COVID-19.

John Nkengasong, daraktan hukumar Afrika CDC ya ce, yawan gwaje gwajen cutar COVID-19 da ake gudanarwa a fadin nahiyar Afrika zai iya kaiwa miliyan 20 nan da karshen watan Oktoban shekarar 2020.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China