Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya bukaci kasa da kasa su taimakawa mutanen dake fama da talauci
2020-10-18 16:36:17        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci kasashen duniya da su taimakawa mutanen dake rayuwa cikin yanayin talauci.

A sakon da ya aike na ranar yaki da talauci ta duniya wacce aka saba gudanarwa a ranar 17 ga watan Oktoba, ya ce, "a wannan rana ta yaki da talauci ta duniya, ya dace al'ummar kasashen duniya su tallafawa mutanen dake rayuwa cikin talauci, a wannan hali da ake fama da annobar COVID-19 har ma bayan annobar."

Jami'in MDDr ya ce, annobar COVID-19 wata masifa ce nau'i biyu ga mutane masu fama da talauci a duniya.

Na farko, matalauta su ne mafiya fuskantar barazanar kamuwa da kwayar cutar, kuma su ne ke da karancin damar samun tsarin kula da lafiya. Na biyu, wani kiyasi da aka gudanar a baya bayan nan ya nuna cewa annobar za ta iya jefa mutane miliyan 115 cikin yanayin talauci a wannan shekarar, wannan shi ne adadi mafi yawa a cikin gwamman shekaru. Mata su ne suka fi shiga hadari saboda sun fi fuskantar barazanar yiwuwar rasa ayyukansu, kuma su ne ke da karancin yiwuwar samun kariya, in ji babban sakataren MDDr. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China