Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba zai yiwu Sin ta shiga wata yarjejeniya ta sassa uku game da kwance damarar makaman nukiliya ba
2020-10-13 10:35:08        cri
Shugaban tawagar kasar Sin, kuma mataimakin wakilin dindindin a MDD Geng Shuang, ya yi watsi da kiran da Amurka ta yiwa kasar Sin, na shiga wata yarjejeniya mai nasaba da kwance damarar makaman nukiliya tsakanin Amurka da Sin da Rasha.

Geng Shuang wanda ya bayyana matsayar Sin a jiya Litinin, yayin da yake jawabi ga mahalarta zaman muhawar kwamiti na farko na zaman babban zauren MDD na 75, ya ce babu adalci a bukatar da Amurka ta bijiro da ita.

Jami'in ya kara da cewa, a baya bayan nan, Amurka ta bayyana Sin a matsayin kasa ta 3 mafi karfin makaman nukiliya a doron kasa, don haka take fatan ita da Sin da Rasha, za su yi wata hadaka ta kulla yarjejeniyar dakile irin wadannan makamai tsakaninsu.

To sai dai kuma wakilin na Sin ya ce, wannan wani yunkuri ne kawai Amurka ke yi, na kawar da hankalin duniya daga muhimman al'amura, da suka hada da bukatar da aka dade ana mikawa mata, na kwance damarar makaman ta na nukiliya, yayin da take kara daukar matakai na neman samun fifiko kan sauran kasashe a wannan fanni.

Geng Shuang ya ce har kullum kasar Sin na bin tsarin amfani da makaman nukiliya ne domin tsaron kai, kuma ba ta taba shiga wata takara ta mallakar irin wadannan makamai tsakaninta da wata kasa ba. Kaza lika duba da babban gibin dake tsakanin Sin da sauran kasashe biyu mafiya karfi a fannin mallakar makaman kare dangi, bai dace a bukaci Sin ta shiga wata yarjejeniyar dakile makaman nata ba. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China