Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi watsi da zarge-zargen Amurka kan COVID -19 da batun kawar da makamai
2020-10-10 17:38:07        cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi watsi da zarge-zargen Amurka kan kasarsa, game da batun COVID-19 da shirin kawar da makamai na duniya, yayin muhawarar kwamitin farko na babban zauren MDD.

Cikin sanarwar da ya fitar, Geng Shuang, ya ce wakilin Amurka ya yi wasu zarge zarge mara tushe kan kasar Sin, har da ikirarin cewa, Rasha da Sin na shirya makaman nukiliya.

Ya ce wakilin Amurka ya yada jita-jita tare da bata sunan kasar Sin dangane da batun annobar COVID-19, wanda abu ne da ba za a lamunta ba ko kadan. Ya ce gujewa daukar nauyi ba zai gyara kurakuran da Amurka ta tafka a yaki da annobar ba, haka kuma ba zata yi wa duniya wayo ba. Ya ce kasar Sin na watsi da zarge-zarge marasa tushe da wakilin Amurka ya yi mata game da mallakar makamai.

A cewarsa, Amurka ce ke babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar duniya.

Har ila yau, ya bukaci Amurka ta shiga ayyukan kwamitin da zuciya daya kuma bisa hanyar da ta dace, ta kuma hada hannu da sauran kasashe wajen tabbatar da nasarar aikin kwamitin da inganta shirin kawar da makaman da kuma kare tsaro da zaman lafiyar duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China