Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mark Lowcock: Al'ummun yankin Sahel ne kan gaba wajen fuskantar matsin rayuwa
2020-10-14 10:04:15        cri
Sakataren MDD mai lura da harkokin jin kai Mark Lowcock, ya ce al'ummun dake zaune a yankunan Sahel na Afirka ne kan gaba, wajen fuskantar matsin rayuwa.

Mark Lowcock wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, cikin jawabinsa ga mahalarta taron da cibiyar nazarin harkokin siyasa ta Faris ta shirya ta kafar bidiyo, ya ce yankin Sahel na fama da tashe-tashen hankula, da rashin tsaro, da raunin shugabanci, da matsanancin rashin ci gaba. Kaza lika yankin na fuskantar yawan matalauta, da matsi na yawan al'umma da sauyin yanayi.

Jami'in ya ce, akwai bukatar gwamnatocin kasashen yankin su kara azama wajen kiyaye sassan yankunansu, musamman ma ta hanyar daukar matakan soji, don murkushe masu tsattsauran ra'ayi, da masu aikata muggan laifuka.

Mr. Mark Lowcock ya lasafta wasu ginshikai 4 da ya ce ya dace a aiwatar da su a yankin na Sahel. Ciki hadda samar da faffadan tallafin jin kai na dogon lokaci, da zuba jari a fannonin samar da hidimomi, musamman fannin ba da ilimi, da kiwon lafiya, da samar da tsaftaccen ruwan sha, da tsaftar muhalli, da kuma tsarin kayyade iyali.

Kaza lika a cewar sa, a fili take cewa, salon gargajiya na rayuwar mazauna wannan yanki da ya kunshi noma da kiwo, ba zai iya daukar nauyin al'ummun dake zaune a wannan yanki ba, don haka akwai bukatar aiwatar da sauye-sauye. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China