Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi kira ga kasashen yankin babban tafkin Afirka da su rungumi matakan zaman lafiya da ci gaba
2020-10-14 10:14:59        cri
Mataimakin wakilin dindindin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kasashen dake kewayen babban tafkin Afirka, da su yi amfani da damar da suke da ita, wajen aiwatar da matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba.

Dai Bing ya ce, a 'yan shekarun baya bayan nan, al'amura a wannan yanki na kara daidaita, an kuma samu dama ta ba safai ba, ta inganta zaman lafiya da ci gaban yankin.

Jami'in ya kara da cewa, Sin na kira ga wadannan kasashe da su gina tsarin cimma manufa guda, da karfafa hadin gwiwa, su kuma mayar da kalubale zuwa damar bunkasa, don kaiwa ga cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da daidaito, da ci gaba na bai daya cikin gaggawa a yankin.

Dai Bing ya ce, kasashen yankin na da makoma ta bai daya, kuma bullar cutar COVID-19 da Ebola, sun haska irin bukatar dake akwai ta karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen.

Ya ce a matsayinta na kawa, kuma abokiyar huldar kasashen dake kewayen babban tafkin Afirka, har kullum Sin na goyon bayan kasashen, a kokarinsu na wanzar da zaman lafiya, tana kuma shiga a dama da ita a ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD a yankin, ta kuma yi duk mai yiwuwa, wajen tallafawa fannin sanin makamar aiki a yankin. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China