Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya bukaci a dauki matakan farfado da halittu dake neman bacewa daga doron kasa
2020-10-01 16:41:51        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, yayi kiran a daura damarar farfado da nau'ikan halittun dake neman bacewa daga doron kasa.

Guterres, ya bayyana a taron kolin MDD kan halittu cewa, kiyaye halittu da kiyaye muhallin halittu suna da matukar alfanu ga cigaban rayuwar dan adam da makomarsa. Wasu muhimman ginshikai ne wajen cimma nasarar samun dawwamamman cigaba da kuma aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris.

Har yanzu, duk da irin jaddada kudiri da ake yi kan batu, amma babu wani cikakken kokari da aka aiwatar domin cimma muradin shirin kare halittu na kasa da kasa da ake burin cimmawa zuwa shekarar 2020. Ya kamata a kara himma, ba wai daga bangaren gwamnatoci kadai ba, har ma da bangarorin masu ruwa da tsaki a cikin al'umma.

Jami'in MDDr yayi gargadin cewa, gurbata tsarin yanayi muhallin halittu ba yana shafar batun muhalli kadai ba ne, har ma yana shafar batutuwan tattalin arziki, kiwon lafiya, hakkokin 'yan adam, da kuma 'yancinsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China