Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya bukaci hadin gwiwar kasa da kasa domin dakile aniyar bata gari dake neman riba ta hanyar cutar COVID-19
2020-10-13 10:51:16        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci hadin gwiwar kasa da kasa a yayin da bata gari ke kokarin fakewa da annobar COVID-19 domin samun riba.

Guterres ya ce, bata gari suna kokarin hada kansu domin neman riba daga annobar COVID-19, ya kamata gwamnatoci su hada kansu don yin aiki tare karkashin tsarin yarjejeniyar MDD domin kawar da laifukan safarar bil adama, da fasa kaurin makamai, da sauran laifukan da ake aikata su wadanda suka ratsa cikin kasashe, jami'in MDD ya bayyana hakan ne a sakon bidiyo na taron kasashen duniya da suka sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa don yaki da muggan laifuka.

Taron na tsawon mako guda, wanda a hukumance shi ne karo na 10 na yarjejeniyar COP, ofishin MDD mai yaki da shan muggan kwayoyi da aikata laifuka ne ya shirya taron.

Kimanin kasashen duniya 190 ne suka amince da shiga yarjejeniyar, ita ce kadai yarjejeniyar da ta hada kasa da kasa domin tinkarar barazanar aikata muggan laifuka. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China