Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane miliyan 7 ne aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Amurka
2020-09-26 15:51:09        cri
Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka ta fitar da wata sabuwar kididdiga game da cutar COVID-19, inda ta bayyana cewa, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya zuwa jiya Juama'a, ya kai sama da miliyan 7, kana yawan wadanda ta yi sanadin mutuwarsu ya kai 203,240.

Amurka dai ita ce kasar da ta fi kowacce yawan masu fama da cutar da wadanda ta yi sanadin mutuwarsu a duniya.

Kididdigar ta nuna cewa, ya zuwa ranar 9 ga watan Augusta, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya zarce miliyan 5, sannan ya zuwa ranar 31 ga watan Augustan, adadin ya zarce miliyan 6. Wato cikin kwanaki 22, adadin ya tashi daga miliyan 5 zuwa miliyan 6, sannan cikin kwanaki 25, ya tashi daga miliyan 6 zuwa 7. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China